Kudin Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan Daya A Watan Agusta - NNPC

Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

Kudin tallafin man fetur na Najeriya ya tashi zuwa naira biliyan 525.714 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.22 a watan Agusta, wanda ya kawo jimillar kudaden da aka kashe a bana zuwa naira tiriliyan 2.568, kamar yadda alkaluman da kamfanin mai na kasar NNPC ya mika wa gwamnati.

WASHINGTON, D. C. - Karuwar farashin kudin tallafi na man fetur a kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a nahiyar Afirka na dagula kasafin kudi da kuma rage kudaden shiga daga Hukumar Man Fetur ta Najeriya (NNPC).

Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

A watan Afrilu ne dai majalisar dokokin Najeriya ta amince da tallafin man fetur na naira tiriliyan 4 na wannan shekara bayan da gwamnati a watan Janairu ta yi watsi da alkawarin kawo karshen tallafin da ta ke bayarwa domin dakile zanga-zanga a lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasa a watan Fabrairun 2023.

Kamfanin mai na kasa NNPC bai mika wa gwamnatin tarayya kudi ba a bana saboda yawan kudaden tallafi.

Kudirin na watan Agusta idan aka kwatanta da Naira biliyan 448.782 a watan Yuli, kamar yadda takardar da NNPC ta mika a ranar Juma’a ga kwamitin raba asusun tarayya.

Hedikwatar NNPC

Wani bangare na karin kudin sakamakon karin yawan man fetur ne na yau da kullum, wanda ya haura zuwa lita miliyan 71.8, kusan kashi 10% daga watan Yuli, a cewar bayanan da hukumar ta Nigerian Midstream da Downstream Petroleum Regulatory Authority ta gabatar.

Yawan man fetur da ake hakowa a cikin watan Agusta ya kai ganga miliyan 1.18 a kowace rana, wanda ya yi kasa da adadin OPEC na kasar da ya kai bpd miliyan 1.8, saboda yawan fasa bututun mai da ke hana hako man.

-Reuters