Kudaden Haram Na Taimakawa Ta'addanci - Kungiya

Kudaden Najeriya

Yin amfani da kudaden fasa-kwauri ko kuma haramtattun kudade, na daga cikin hanyoyin da wasu bi domin yin ayyukan ta'addanci.

Wata kungiya mai rajin kare kudaden jama’a da ake kira KIAPA, ta gudanar da wani taro domin wayar da kan jama’a kan illar da kudaden fasa -kwaurin kudade ke yi wajen taimakawa ayyukan ta’addanci.

Yayin da ya ke jawabi a wajen bude taron, shugaban wannan kungiya, Adama Coulibaly, ya ce masu ayyukna ta’addanci na amfani da irin wadannan kudade musamman ma a nahiyar Afrika, inda y ace hakan na barazana ga nahiyar ta fuskar saka jari da sauran ayyukan raya kasa daga kasashen ketare.

Shi kuwa Darekta hulda da jama’a na kungiyar cewa ya yi, ta hanyar amfani da wadannan kudade na haramun ake samun rikice-rikice a nahiyar.

“ Akwai wani rahoto da muka fitar a shekara ta 2013, wannan rahoto ya nuna ainihin hanyoyin da ake amfani da su wajen irin wadannan munanan ayyuka, mun ba da wannan rahoto saboda kasashe irinsu Najeriya da Nijar za su sami ainihin bayanai domin su yi aiki da su.” In ji Timothy Mai Laya.

Wani mai yiwa kasa hidima, wanda ya halarci taron, ya ce lallai ana amfani da matasa ta inda ake ba su kudade a lalata rayuwarsu, yana da kyau matasa su dinga duba inda kudade su ke fitowa da kuma abin da ake so mutum ya yi.”

Ga karin bayani game da wannan labari.

Your browser doesn’t support HTML5

Kudaden Haram Na Taimakawa Ta'addanci - Kungiya 4'27"