WASHINGTON D.C —
Ruth Dominic matashiya 'yar asalin jihar Akwai Ibom , kuma wacce ta kammala karatun sakandare kuma take da burin komawa makarantar gaba da sakandire domin karo ilimi.
Matashiyar ta ce tana sana'a ne domin ta tara kudin karatun ta amma tana fuskantar wasu matsaloli wajen tara kudin, a cewarta ba'a biyanta kudin albashin ta akan lokaci harma wani lokaci sai an shiga sabon wata.
Ta dalilin haka ne ta yi kira ga 'yan mata matasa da magidanta su tashi tsaye domin kama sana'a da kuma karo ilimi domin dogaro da kai,
Daga karshe ta bayyana cewa rashin biyan ta akan lokaci ba karamin nakasu bane musamman ga yadda ta ke dogaro akan abinda ake biyan ta da kuma burin ta a rayuwa.