Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasahar Facebook Mai Suna Safety Check Ta Sami Tangarda


Wata fasaha da shafin Facebook suka kirkiro wadda zata baiwa mutum damar sanar da abokansa cewa yana lafiya bayan afkuwar wani abin tashin hankali a inda mutum yake, ta samu tangarda a bayan fashewar bom a Pakistan ranar Lahadi.

Kamar yadda kamfanin yada labarai na NBC ya rawaito, yace mutane dayawa a Amurka da Turai sun sami sakon da yake tambayarsu ko suna lafiya bayan fashewar bom a Lahore da ya kashe sama da mutane 70.

Sakonnin dai sun isa ga jama’a ta hanyar sakon karta kwana wato text massage, inda suke tambayar idan fashewar bom din ya shafesu, amma bai ambaci kasar Pakistan ba. sai dai sakon da ya fito ta kwamfuta yace bom din ya tashi a garin Lahore.

A wata sanarwa da kamfanin Facebook ya fitar tace, “abin mamaki yawancin mutanen da suka sami wannan sakon ba wanda abin ya shafa bane kuma yana tambayarsu ko suna lafiya.” Ta ci gaba da cewa muna neman afuwa ga duk wanda ya sami wannan sakon bisa kuskure.

Ita dai wannan fasaha da ake kira Safety Check anyi ta ne domin masu amfani da shafin Facebook su sanar da abokansu cewa suna lafiya, alokacin da wani abu ya faru a yankin da suke, kamar harin ta’addanci da aka kai birnin Paris a Faransa.

Sai dai kamfanin na shan suka kan yadda wani lokaci bata aikin da ya kamata, missali cikin watan Nuwamba bom ya fashe a Najeriya, amma ta dauki awanni kafin ta aika da sakonni.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG