Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aika karin sunayen mutum 19 a matsayin wadanda zai nada ministoci a gwamnatinsa.
Hakan ya kawo jimullar adadin sunayen da ya aikawa majalisar zuwa 47. A makon da ya gabata, Tinubu ya aika da sunaye 28.
A wannan karon sunayen da suka fi jan hankali cikin wannan jeri na biyu, sun hada da tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Filato Simon Lalong da tsohon gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam.
Ga cikakken jerin sunayen da ya aika a wannan karo:
Abdullahi Tijjani Gwarzo, Bosun Tijani, Dr Maryam Shetty, Isiak Salako, Tunji Alausa, Dr Yusuf Tanko Sununu, Adegboyega Oyetola, Atiku Bagudu, Bello Matawalle da Ibrahim Geidam.
Sauran sun hada da Simon Lalong, Lola Ade John, Shuaibu Abubakar Audu, Prof Tahir Mamman, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, Sanata Alkali Ahmed Saidu, Sanata Heineken Lokpobori, Uba Maigari Ahmadu da Zaphaniah Bitrus Jisalo.