Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a jihar Bauchi ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar, Barista Muhammed Abdullahi Abubakar, suka shigar.
Tsohon gwamnan da jam'iyyarsa, sun kalubalanci nasarar da jam’iyyar PDP ta samu wanda dan takararta, Sanata Bala Muhammed Abdulkadir, ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Bauchi.
Kotun karkashin shugabancin mai shari’a, Salihu Shu’aibu, da wasu alkalan guda biyu masu dafa masa sun bayyana cewa karar ba ta da inganci sannan masu karar sun gaza tabbatar da abubuwan da suke zargi game da zaben.
Shugaban kotun sauraron karar zaben, Salihu Shu'aibu, ya shafe sama da sa’o’i shida yana karanta hukuncinsa wanda wakilan bangarorin suka halarta, inda ya ce zaben da aka yi na gwamna sahihi ne mai cike da gaskiya, sabili da haka kotu ta tabbatar da Sanata Bala Muhammed Abdulkadir, a matsayin gwamnan jihar Bauchi.
Bayan yanke hukuncin mutanan da suke wajen kotun sun barke da shewa da kuma kade kade, domin nuna farin cikinsu da hukuncin.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:
Your browser doesn’t support HTML5