Kotun Tarayyar Amurka Ta Hana Karin Kudin Cika Takardun Shiga Amurka

Hana aiwatar da matakin karin ya hada da sanya dala 50 don cika takardun neman mafaka a kasar, wanda da ya zama karon farko da Amurka zata caji kudi kan wannan.

Wata kotun tarayya a Amurka ta hana karin kudin cika takardun da suka shafi shiga Amurka da neman zama kasar da ya kamata ya fara aiki a wannan makon.

Ranar Juma’a ya kamata karin na kusan kashi 20 cikin 100 ya fara aiki dangane da irin takarda ko izinin da ake bukata.

Hana aiwatar da matakin karin ya hada da sanya dala 50 don cika takardun neman mafaka a kasar, wanda da ya zama karon farko da Amurka zata caji kudi kan wannan. Sai kuma cika takardar neman zama dan kasa da aka kara daga dala 640 zuwa dala 1,170.

Wadanda ke neman takardun daga iyalai masu karamin karfi na iya neman a dage musu biyan kudin, amma sabbin matakan da ya kamata su fara aiki ranar Juma’a sun kawar da wannan damar, ta nuna cewa suna fuskantar matsalar kudi mai tsanani.

Hukumar harkokin shigi da fici da zama dan kasa ta Amurka da ake kira USCIS a takaice, da ke yin aiki kan takardun visa, da neman mafaka, da zama dan kasa da sauran abubuwa, ta bayyana cewa an samu raguwa sosai a kudaden da ke shiga na ma’aikatar a farkon shekarar nan saboda annobar cutar coronavirus har a wani lokaci ta so ta dakatar da ma’aikatan da yawa na wani dan lokaci.

Ma’aikatar ta USCIS na samun kudin gudanar da harkokinta ne yawanci daga kudaden da take karba daga masu neman izinin shiga, ko zama ‘yan kasa, ba kamar sauran ma’aikatun gwamnatin tarayyar kasar ba.