Kotun Tarayya Ta Rushe Babban Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Yi A Watan Mayu

PDP

A Abuja wata kotu ta soke babban taron da jam’iyyar PDP ta yi a watan Mayu, wanda ya baiwa Sanata Ahmed Makarfi shugabancin jam’iyyar.

Hukuncin babbar kotun tarayyar dai ya biyo ‘daukaka ‘kara ne da Sanata Ali Modu Sheriff ya yi dake bukatar kada a taba kujerarsa gabanin sahihin babban taron jam’iyyar. Kotun dai ta soke babban taron da jam’iyyar ta yi a Port Harcourt a watan Mayu, wanda shine ya karkare da kafa kwamitin Sanata Ahmed Makarfi.

Alkali Okon Abang, yace gabanin taron na Port Court akwai umarnin babbar kotun tarayya ta Lagos sau biyu da ya hana taba kujerar ta Sheriff.

Wasu matasa masu marawa Ahmed Makarfi baya, sun gudanar da zanga zanga zuwa babbar kotun tarayyar don hana hukuncin da hakan bai samu karbuwa ba. Mai taimakawa Sheriff kan labaru Inuwa Bwala, yace abin da ya faru yau ya nuna gaskiyar abin da Sheriff yace akai, shine maganar gaskiya, bin doka, shine kuma tsayayyar maganar da yace akwai a gaban doka.

Wannan dai ya nuna kokarin sulhun da kwamitin amintattun PDP na dakatar da shari’ar a kotu ya ci tura. A cewar shugaban kwamitin amintattun Sanata Walid Jibrin, ana nan ana ta kokarin ganin kwamitin ya samu hanyar da zata dinke banbance banbancen da ke cikin jam’iyyar.

Hukumar zabe dai ta amince da tafiya da bangaren Makarfi a lamuran PDP gabanin zuwan wannan hukuncin, dake nuna komai na iya sauyawa bisa matakan shari’a.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Tarayya Ta Rushe Babban Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Yi A Watan Mayu - 2'58"