Wata kotu a Sifaniya ta yankewa tsohon dan wasan Kamaru Samuel Eto’o hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 22 bayan da aka same da laifin kaucewa biyan kudaden haraji a lokacin yana bugawa kungiyar Barcelona wasa.
Sai da hukuncin na je-ka-gyara-halinka ne kamar yadda AP ya ruwaito.
A Sifaniya, hukuncin zaman gidan yari da ya gaza shekara biyu, kan zama na je-ka-gyara-halinka ga wadanda aka samu da laifi a karon farko.
Cikin wata yarjejeniya da aka kulla da hukumomin harajin kasar, Eto’o zai mayar wa kasar ta Sifaniya dala miliyan 4.2 da aka biyo shi bashi kan haraji.
Eto’o, wanda ya amince da hukuncin, ya dora laifin aukuwar hakan akan wakilinsa Jose Maria Mesalles.
Kotun ta yankewa Mesalles hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara daya.
Dan shekara 41, Eto’o ya bugawa Barcelona wasa daga shekarar 2004 zuwa 2009, inda ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Zakarun Turai sau biyu da kofin gasar La Liga uku.