Bayan an bayar da belin din Kwamarad Bashir Dauda, yace rubutun da yayi ba rubutu bane na batanci ko karya ga wani ba, ya bayyana ra’ayinsa ne kawai kan cewa talakawa na shan wahala idan aka duba yadda abinci ke yiwa mutane wahala, kuma ana dadewa ba a biya mutane albashi ba a jihohi da dama a fadin Najeriya. haka kuma Bashir ya sha alwashin ci gaba da yin rubutunsa bisa gaskiya da kuma hujjoji.
Ga alama dai kafofin sadarwa na sada zumunci na neman zama wani sabon babban kalubale ga gwamnatoci a Najeriya, ko da yake suna dauke da alfanun da ke tattare da su. Babban jami’i a cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma dake birnin Kano, Kabiru Sa’idu Dakata, yayi magana kan yadda shugabannin kasar sukayi amfani da hanyoyin sadarwa, amma wasu gwamnatocin na kokarin dakilewa mutane hakin fadin albarkacin baki.
To amma Barista Abdu Bulama na kallon lamarin ne ta fuskar shari’a, bisa tanadin dokokin kasa dama yarjejeniyoyin kasa da kasa da Najeriya ta rattabawa hannu. Inda yace dole ne a dimokaradiyya a baiwa mutane dama su kalla abubuwan da gwamnati ke yi, su kuma fadi ra’ayinsu a kai, kuma in aka ce an hanasu wannan to dole ne a fuskanci matsala.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5