Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Kungiyar Boko Haram Na Yiwa Yankin Askira Uba Barzana


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Duk da cewa an kwato wuraren da kungiyar Boko Haram ta mamaye can baya a jihar Borno, har yanzu kungiyar na kai hari jefi jefi a wasu wurare irin su yankin Askira Uba kamar yadda shugaban maharban yankin ya shaida

Musa shugaban kungiyar maharba na yankin Askira Uba ya shaidawa Muryar Amurka irin abun da suke fama dashi da harin jefi jefi na 'yan Boko Haram.

A garin Wamdio suna ci gaba da fama da 'yan ta'adan. Kwana kwanan nan 'yan Boko Haram suka kashe masu yara hudu wasu kuma sun bace ba'a san inda suke ba. Can baya 'yan kungiyar sun zauna a garin inda suka kashe mutane da dama kodayake basu yi kone kone ba. Yanzu matasan sun tashi su kare garinsu.

Kawo yanzu mutanen suna korafi kan cewa babu wani tallafi da suka samu, walau daga gwamnatin tarayya ko ta jiha.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG