Kotun Kolin Amurka Ta Goyi Bayan Wata Manufar Trump Kan Baki

Kotun kolin Amurka ta amince da cewa masu neman mafaka a Amurka ba za su iya kalubalantar shirin maida su kasashensu na asali a kotunan tarayya ba, alkalai 7 ne suka kada kuri’ar amincewa 2 kuma suka yi akasin haka, abinda ya ba gwamnatin Trump nasara a kokarin da ta ke yi na takaita manufoffin kasar da suka shafi shige da fice.

A takardar da ya rubuta, alkali Samuel Alito ya ce masu neman mafaka a Amurka wadanda hujjojin da suka gabatar ba su samu karbuwa a binciken farko da jami’an hukumar shige da fice suka yi ba, ba su da ikon kai batun gaban wani alkali kuma ana iya tusa keyarsu a maida su kasashensu cikin sauri. Alito ya bayyana tsarin a matsayin ‘fidda masu neman mafaka da ba su cancanta ba.”

Kotun ta yanke hukuncin ne a shari’ar Vijayakumar Thuraissigiam, wani dan kabilar Tamil da ke Sri Lanka, wanda ya ce ya bar kasarsa ne bayan da wasu bata gari suka yi masa duka.

Jami’an gwamnatin tarayya sun mika Thuraissigiam a hannun Hukumar tsaron Amurka a California da ke mita 25 arewa da iyakar Amurka da Mexico.

Jami’an sun yanke hukuncin cewa Thuraissigiam bai bada kwararan hujjojin da suka nuna fargaban za a kuntata mashi idan aka maida shi Sri Lanka ba haka kuma ya cancanci a fidda shi daga Amurka.

Thuraissigiam ya kai kara, inda ya zargi gwamnatin kasar da hana shi damar a duba kokensa.