Kotun Koli Tayi Watsi Da Daukaka Karar Gwamnan Jahar Rivers

Gwamna Wike baida hujjar kalubalantar hurumin karamar Kotun

Kotun kolin Najeriya, tayi watsi da daukaka karar da Gwamnan jahar Rivers, Nyesom Wike,yayi da jam’iyyar sa ta PDP, inda suke kalubalantar maido da zaman kotun sauraren kararrakin zaben na jahar Rivers, zuwa Abuja.

Cikin hukuncin da kotun kolin ta yanke tace Gwamna Wike, baida wata huja na kare wannan daukaka kara nashi.

Mai Sharia Amiru Sanusi, daya karanta hukuncin ya zartar da cewa zaman kotun sauraren kararrakin jahar Rivers din a Abuja, bai sabawa dokar Najeriya, ba dan haka Gwamna Wike baida hujjar kalubalantar hurumin karamar Kotun.

Wani Lauyan tsarin milki a Najeriya, Barrister Mainasara Kogo Ibrahim, ya ce a gane wannan hukuncin Kotun kolin daban ne bawai daukaka kara bane kan hukuncin rushe zaben Gwamna Wike.

Barrister Mainasara ya ce bisa kundin tsarin milkin Najeriya, Gwamna Wike zai ci gaba da zama Gwamnan jahar Rivers, har sai an yanke hukunci idan ya daukaka kara.

A dai jahar Rivers, a ‘yan tsakanin nan sai da Kotun sauraren kararrakin zaben ta soke zaben kakakin Majalisar dokokin jahar da wasu ‘yan Majalisar guda 20.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Koli Tayi Watsi da Daukaka karar Gwamnan Jahar Rivers - 1'37"