A yau ma dai Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Mohammed, wandan shi ne ya jagoranci lawyoyi bakwai da ke sauraren shari'ar zabukan gwamnonin jihohi bakwai har da na Kano da Sokoto, ya sake daga ranar da za su yanke hukunci akan zaben gwamnan Jihar Kano.
Wannan shi ne karo na uku da kotun koli ta dage shari'ar zaben gwamnan Jihar Kano zuwa ranar Litinin 20 ga wannan wata na Janairu.
Kwamitin alkalai 7 a karkashin jagorancin babban Alkalin Tarayya, Jusitce Tanko, ya yanke shawarar sake dage yanke hukunci akan karar saboda bukatun da Lauyoyin Ganduje, da na Abba Gida-Gida suka gabatar a gaban Kotun.
Daya daga cikin lauyoyin Ganduje Musa Abdullahi Lawal ya bayyana cewa yadda suka yi ta nanantawa dai ba za ta canza zani ba saboda su 'yan PDP suna korafi ne cewa da an ayyana wanda ya ci zabe a ranar 9 ga wata, da ba a yi "Inconclusive" ba har a maimata zabe a wasu mazabu.
Ya ce kuma abin lura shi ne, wasu wurare da aka sake zaben akwai inda masu rajista suka kai dubu 40, wanda ya nuna cewa sun fi yawan kuri'un da aka ce yana tsakanin 'yan takaran su biyu.
Saboda haka, su suna da yakinin cewa Ganduje ya lashe zabe kuma zai ci gaba da zama gwamnan Kano.
Amma ga Barr. Ibrahim Isa Wangida wanda ya ke cikin tawagar dan takarar PDP Abba Gida Gida, yana ganin wannan kotun koli ita ce kotun "Allah ya isa" saboda haka suna da yakinin za ta gyara kurakuran da kotunan baya suka yi a baiyana sakamakon za6en.
Kenan za su lashe amansu a ranar 20 ga wannan wata su bayyana Abba Gida Gida a matsayin wanda ya ci zaben Kano.
Magoya bayan APC irin su Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, sun ce Ganduje ne ya lashe zaben Kano kuma rana ba ta karya, suna masu fatan a ranar 20 ga wannan wata haka za bayyana.
Shi kuma Ali Madakin Gini mai goyon bayan Abba Gida Gida, yana ganin a ranar 20 ga wata za a bayyana Abba a matsayin wanda ya ci zaben Kano.
An dage hukuncin jihohin Binuwai, Filato, da Bauchi su ma sai nan gaba.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5