Kotun Koli Ta Ba Trump Damar Gina Katanga Tsakani Da Mexico

An samu rabuwar kawuna tsakanin alkalan kotun kolin Amurka 5 da 4, inda alkalai biyar suka amince da baiwa shugaban Donald Trump billiyoyin da ya bukata, don cika alkawalin da yayi na gina Katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico.

Hukuncin na jiya Juma’a, ya warware matsayar wata karamar kotu da ta saka takunkumi, akan wasu kudade da suka kai dala biliyan $2.5 na ma’aikatar tsaro.

“Babbar nasara akan tsaron bakin iyaka, da bin doka” shugaba Trump kenan ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Wani lauya Dror Ladin, na kungiyar American Civil Liberties Union National Security Project, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na French News Agency, cewar al’ummar da ke kusa da bakin iyaka, da sauran jama’a, harma da kundin tsarin mulkin kasar mu zasu ga bai dai-daiba.

Muddun akace Trump ne shugaba kasar, kuma idan ya iya samun nasarar taba kudaden da aka ware don tsaro, don cinma wani burin sa na kinjin, duk da cewar ‘yan majalisu sun ki amincewa da shirin.