Kotun Jihar Enugu Ta Samu Wasu Mutane 17 Da Laifin Zamba Ta Intanet

Wasu daga cikin mutanen da kotu ta samu da laifin zamba ta intanet a jihar Enugun Najeriya (Hoto: Facebook/EFCC)

A ranar 18 ga watan Mayun 2022, Mai shari’a Ibrahim Buba ya yanke masu hukuncin bayan gurfanar da su da hukumar EFCC ta yi a gaban kuliya.

Wata kotun tarayya a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta samu wasu mutane 17 da laifin gudanar da ayyukan da suka shafi yin zamba ta kafar intanet.

Hukuncin ya biyo bayan da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa kasa zagon kasa da ke Abuja, ta tusa keyarsu zuwa kotun kamar yadda hukumar ta EFC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis.

A ranar 18 ga watan Mayun 2022, Mai shari’a Ibrahim Buba ya yanke masu hukuncin bayan gurfanar da su da hukumar EFCC ta yi akan laifi mai alaka da zamba ta intanet.

Ku Duba Wannan Ma Yadda EFCC Ta Gurfanar Da Rochas Jim Kadan Bayan Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023 

Masu laifin sun hada da Aguoha Ujunwa, Samson Ebuzoeme, Iwuji Kelechi John Kennedy, Onyeanu Kinsley, Emmanuel Udo, Mmesoma Emmanuel, Prosper Chizaram Ugochukwu, Chima Chibuike Kingsley, Nzeadi Chika Camillus, Nwaugu Nzubechi Bethel.

Sauran su ne, Opara Ikenna Christopher, Chindorom Gideoan Ehimere, Okoroafor Samuel and Obaa Emeka Ama, Osinachi Goodness Nwokore, Smart Clinton Onyinyoma, Iheanacho Ikenna, Chinonso Henry Ogu da Anyanwu Foxby.

Sha bakwai daga cikin 19 da aka gurfanar sun amsa laifin na su, inda mai shari’a ya yanke musu hukuncin zama gidan gyara halinka ko su biya tarar kudi naira miliyan daya ga kowannensu.