A shekarar 2017, Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Ƙasa EFCC ta kai samame wani gidan Yakubun da ke Sabon Tasha a Kaduna inda tae ta gano dala miliyan 9.7 da fam 74,000 a cikin wani ma’aji
Daga nan EFCC ta shigar da karar cewa Yakubu ya samu kudin ne ta hanyar da ba ta dace ba kuma kudin ba su bi ta banki ba.
Andrew Yakubu ya shaidawa kotu cewa kudin sun taru ne daga kyaututtukan da ya samu daga abokan sa bayan ajiye aiki a 2014.
Yakubu ya ce ya tara kudin ne a waje daya da kadan-kadan ba wai a dunkule ya same su ba.
Mai shari’a Ahmed Muhammed ya yanke hukuncin wanke Yakubu da umurnin a mayar ma sa kudin sa don kotu ta gamsu da hujjojjin da Yakubu ya gabatar.
Kotun ta ce EFCC ta gaza bincika gaskiyar an tara kudin ne da kadan-kadan kuma ba ta taba kawo kudin gaban kotun ba tun fara shari’ar.