Kotun ICC Ta Samu Ntaganda Da Laifukan Yaki

Ntanganda wani lokaci a can baya da ake sauraren kararsa

A yau Litinin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta samu tsohon shugaban ‘yan tawayen kasar Congo, Bosco Ntaganda da laifukan yaki 18 da ake tuhumar shi da su da kuma aikata laifi akan bil’adama.

Ntaganda ya musanta cewa ya kashe mutane kuma ya aikata laifin yaki a lokacin da aka ba shi dama ya yi magana a zauran shari’ar a ranar Alhamis.

A lokacin da alkalin kotun ICC yake jawabi, Ntaganda ya amince kamar yadda ake mai inkiya da sunan “mai kashewa” amma ya ce “ba haka na ke ba.”

Ntaganda ya dage cewa shi soja ne a lokacin, ya kuma kara da cewa shi ba mai aikata laifi ba ne, inda ya ce, “ni ban taba kai hari kan fararan hula ba. A ko da yaushe ina kare su ne.