WASHINGTON, D.C —
Alkalai a Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, sun ce masu gabatar da kara zasu iya ci gaba da gudanar da bincike kan laifukan yakin da dukkan bangarori suka aikata a yakin Afghanistan.
Wata karamar kotu ta hana wannan yunkurin a bara, tana cewa kamata ya yi kotun ta maida hankali kan kararrakin da za su bada damar kai ga gurfanar da wadanda ake tuhuma.
Kasar Amurka ta nuna rashin amincewa da yunkurin binciken laifukan yaki a Afghanistan, kuma ba ta amince da kotun ta ICC ba.
Afghanistan ma ta nuna rashin amincewa da matakin, tana mai cewa za ta gudanar da nata binciken.
Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun yaba wa ICC a kan kare hakkin wadanda lamarin ya shafa.