Kasashen da suka hada da Chile da Hungary da Poland da kuma Slovenia dukkansu sun bayyana bullar cutar a cikinsu jiya Laraba.
Batun a kasar Hungary ya shafi wasu dalibai biyu ‘yan kasar Iran, yayin da a Slovenia kuma, wanda ke dauke da cutar ya taba tafiya ne zuwa Morocco da Italiya.
Kasar Italiya dai ita ce kasar Turai da ta fi kowacce yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus, inda su ka kai 2,700 baya ga mutum 100 da cutar ta kashe.
Gwamnatin kasar dai ta yanke shawarar rufe duk makarantun kasar har zuwa ranar 15 ga watan Maris.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a taron manema labarai da ya ke gudanarwa kullum kan cutar cewa yanzu haka kasashe 75 ne ke fama da cutar a fadin duniya
Facebook Forum