Kotun Daukaka Kara Tayi Watsi da Bukatar Bukola Saraki

Sanata Bukola Saraki

Kotun daukaka kara dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya tayi watsi da bukatar Sanata Bukola Saraki wanda kuma shi ne kakakin majalisar dattawa.

Kotun tayi watsi da bukatunsa ne akan cewa bata da hurumin tsoma bakinta a batun da ba'a riga an warware ba.

Sau biyu shugaban majalisar dattawan na kin bayyana gaban kotun da'a dake zarginsa da bada bayanan karya bisa ga kaddarorinsa har ma mai shari'a Yakubu Danladi Umar alkalin kotun ya ba babban sifeton 'yansanda umurnin kamoshi.

Akan cigaba da zama shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Tukur El Sudi mai baiwa Sanata Saraki shawara ta fannin shari'a yace babu wani daga waje da yake da ikon ya cireshi daga kan kujerarsa sai dai iadan 'yan majalisa din ne suka cireshi.

A cewar El-Sudi tuhumar da ake yiwa Sanata Saraki ta zama siyasa. Yace tun watan Janairu na wannan shekarar batun Sanata Saraki shi ne kadai a gaban kotun da'ar. Dalili na biyu wai laifin ya yishi ne tun shekarar 2003. Doka ta tanadi cewa idan mutum ya aikata laifin kuma an tabbatar ana iya cireshi daga mukamin a kwace kaddarorin da aka san ba na gaskiya ba ne kana a hanashi rike wani mukami har na tsawon shekara goma.

Bayan shekaru 13 da aikata laifin tambaya nan ita ce menen ma'anar tuhumarsa yanzu. Yayi laifin ne yayinda yake gwamna. Yanzu shi sanata ne. Yaya ke nan?

To amma a wata sanarwa da Sanata Bukola Saraki ya rabawa manema labarai da yammacin jiya yace zai gurfana gaban kotun da'ar ma'aikata yau ba sai 'yansanda sun kamoshi ba. Yace zai yi hakan ne bisa ga shawarwari da lauyoyinsa suka bashi.

Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Daukaka Kara Tayi Watsi da Bukatar Bukola Saraki


.