Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Natasha A Matsayin Saneta

Natasha Akpoti-Uduaghan

Kotun daukaka kara da ke zama a birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduaghan ta Jam’iyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaben Majalisar Dattijai mai wakiltar Kogi ta Tsakiya

Kotun ta goyi bayan soke zaben Sadiku-Ohere na jam’iyar APC da a farko Hukumar INEC ta sanar a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

'Dan takaran na jam’iyar APC ya garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar soke zaben shi da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yi, sai dai ya sake shan kaye.

Da yake yanke hukumci a kotun daukaka karar, Mai Shari’a Hamma Barka ya yi fatali da karar da yace bata da tushe. Ya kuma jadada cewa, hukumcin da kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke ya yi daidai, da ta ba Natasha nasara sabili da tabbatar da danne kuri’un da ta samu a wadansu runfunan zabe a Kogi ta Tsakiya.

Natasha Akpoti-Uduaghan

Kotun ta kuma umarci wanda ya shiga da karar ya biya Natasha Naira dubu dari biyar sabili da wahal da ita.

Tun farko, Hukumar Zabe INEC ta ayyana dan takarar jam’iyar APC Abubakar Sadiku-Ohere a matsayin wanda ya lashe zabe, amma kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kogi ta soke zabe tare da sanar da Natasha Akpoti-Uduaghan a matsayin wadda ta lashe zaben.

Natasha Akpoti-Uduaghan da Yahaya Bello

Jim kadan bayan sanar da hukumcin kotun, gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello na Jam’iyar APC ya taya Natasha murna ya kuma yi kira ga al’ummar jihar su rungumi kadara su bata goyon baya domin ci gaban jihar.

Ku Duba Wannan Ma Kawo Yanzu Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Najeriya Ta Kori Yan Majalisar Dattawa 7 Da Na Wakilai 26