A cikin watan Nuwanban wannan shekara ne ake sa ran kotun koli ta Najeriya za ta kawo karshen takaddamar shari'ar kujerar Sarkin Gwandu, wadda Sarki na goma sha tara Mustapha Haruna Jakolo ya shigar.
Wannan na zuwa ne lokacin da kotun daukaka kara mai zaman ta a Sokoto ta sake bayar da umurnin a mayar da Sarkin a kan karagar mulki tare da biyan shi dukkan hakkokinsa.
Tun a shekarar 2005 ne aka fara shari'ar a babbar kotun da ke Birnin Kebbi, wadda ta yanke hukuncin cewa ba'a bi ka'ida ba wajen tube Sarkin Gwandu na 19, Alhaji Mustapha Haruna Jakolo ba.
Kotun ta yanke hukuncin da a mayar da Sarki Mustapha Jakolo a kan karagar sa a kuma biya shi dukkan hakkokinsa.
Sai dai a wancan lokacin Gwamnatin jihar Kebbi ta daukaka kara zuwa wasu kotuna har guda uku, wadanda dukkan su suka bai wa Jakolo nasara.
Amma daga bisani aka sake daukaka kara zuwa kotun koli, wadda bisa wasu dalilai ta sake mayar da karar a kotun daukaka kara mai zama a Sokoto, wadda kuma ta sake tabbatar da hukuncinta na farko, wanda shi ne tabbatar da hukuncin babbar kotun Birnin Kebbi.
Mr. Pascal C. Onyenobi shi ne lauyan Sarki na 19, Mustapha Haruna Jakolo, ya ce bai yi mamaki ba hukuncin na kotun domin sau uku kuma karo na biyu a wannan kotun ta daukaka kara suna samun galaba.
Lauyan Gwamnatin jihar Kebbi ya ki ya yi magana da manema labarai a harabar kotun, a kan haka na tuntubi Masarautar Gwandu.
Sai dai kafin hada wannan rahoto Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin masarautar da gwamnatin jihar Kebbi amma abin ya ci tura.
Wani na hannun daman Sarkin Gwandu na 19, Aminu Mayana ya bayyana godiya ga Allah a kan wannan galaba da suka samu har sau uku a kotu.
Yanzu dai da wannan hukuncin na kotun daukaka kara karo na biyu, kotun koli ce kawai ta yi saura ta yi nata hukunci a kan karar.
Lauyan Sarki Mustapha Jakolo ya ce kotun koli ita ce raba gardama kuma za ta zartar da na ta hukunci a ranar 25 ga watan Nuwanba na wannan shekara, saboda haka yanzu a iya cewa kallo ya koma kan kotun kolin nan da wata daya mai zuwa.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5