'Yan takarar biyu sun bukaci kotun ta tilasta wa hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ba su damar duba kayan zaben da aka yi amfani da su, ciki har da sakamakon da na'urar BVAS ta dauko don su dauki hujjojin da zasu gabatar wa kotu a karar kalubalantar zaben.
Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ta bude babin shigar da karar kalubalantar sakamkon zaben shugaban kasa da kan fara daga kotun daukaka kara ya kare a kotun koli.
Mai taimaka wa jam'iyyar PDP a fannin yada labarai, Yusuf Dingayadi, ya ce hurumin da kotu ta basu abin farin ciki ne da zai taimaka musu wajen samo kwararan hujjoji da zasu gabatar wa kotu don neman a soke nasarar da Bola Tinubu na APC ya samu.
Ya kara da cewa suna sa ran za a gano kurakuran da aka yi a lokacin zabe, da kuma yadda aka kauce wa tsarin hukumar zabe.
Dingyadi ya ce su na da yakini da kwarin gwiwar samun hujjoji masu inganci da zasu tabbatar da ikirarinsu na cewa an yi magudi sosai a zaben.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:
Your browser doesn’t support HTML5