Kotu Ta Yi Fatali Da Shari’ar Yara Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Yara Masu Zanga-Zanga Da Aka Tsare Na Kusan Kwana 90 - Kotu Ta Yi Fatali Da Shari’ar

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta yi watsi da karar da ake tuhumar gomman kananan yaran nan da ake zargi da laifin cin amanar kasa wadanda aka tsare na kusan kwana casa’in sakamakon shiga zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa inda suka daga tutar kasar Rasha

Duk da cewa gomman yaran da ake tuhumar ba su halarci zaman kotun ba, alkalin kotun, Mai shari’a Obiora Egwuatu, a ranar Talata, ya yi watsi da karar da ake tuhumar su a kai ne biyo bayan bukatar da babban lauyan gwamnatin tarayya, M. D Abubakar ya gabatar na karbar ragamar shari’ar da kuma janye karar, daga bisani alkalin kotun ya ba da umarnin a gaggauta sakin yaran ba wasu sharudda daga gidan yari da suke garkame.

Haka kuma, babban lauyan gwamnatin tarayya Lateef Fagbemi mai mukamin SAN wanda ya samu wakilcin daraktan shigar da kara na kasar.

Mohammed Abubakar, a wajen zaman ya bayyana yin amfani da ikon da dokar kasa ta ba shi, sashe na 174 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 kamar yadda aka yi kwaskwarima na karbar ragamar karar daga hannun babban Sufeton ‘yan sandan kasar, Kayode Egbetokun.

Daga bisani bayan amincewa da bukatar na babban lauyan gwamnatin Najeriya da mai shari’a Egwuatu ya yi, shi babban lauyan gwamnatin ya kara yin amfani da sashen nan na 174 na kundin tsarin mulkin kasar ya katse shari’ar wadanda ake tuhuma kan zanga-zangar 119.

Bayan rashin wani jayayya daga lauyoyin yaran da al’amarin ya shafa a hukuncin kotun nan take, mai shari’a Egwuatu ya amince da bukatar kuma ya yi watsi da tuhumar.

A ranar Litinin din nan ne shugaba Bola Tinubu ya baiwa babban lauyan gwamnatinsa, Lateef Fagbemi, umarnin ya janye tuhumar da ake yi wa wadandan ake zargin da akasarinsu kananan yaran da suka shiga zanga-zangar lumana na neman kawo karshen tsadar rayuwa.

Yaran da suka shafe sama da kwanaki 80 a garkame cikin munin yanayi kuma dokar kasa ta hana yaran nan fuskantar irin wannan shari’a.

Idan Ana biye da labarin, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris wanda ya bayyana umarnin shugaban kasa, ya bayyana cewa Tinubu ya ba da umarnin a saki yaran nan take ba tare la’akari da tsarin shari’a da ke gudana ba.

Shugaba Tinubu ya kuma umurci ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da rage radadin talauci da ta gaggauta duba halin da kananan yara ke ciki ya kuma umarce ta da ta tabbatar da haduwarsu da iyayensu ko masu kula da su a duk inda suke a kasar nan take.

Daya daga cikin lauyoyin dake kare yaran, Barr. Hamza Nuhu Dantani ya tabbatar da sakin kananan yaran nan tare da nuna farin cikin sa da saura abokan aikin sa a kan wannan nasarar su a kan shari’ar yana mai cewa babban sufetan ‘yan sandan Najeriya da ya bada umarnin dauko yaran daga Kano, da Zari’a ya sabawa doka kuma dole ne ya nemi gafarar yaran da iyayensu.

Shi ma Barr. Abubakar Ibrahim Na-jirgi ya tabbatar da hukuncin kotun na yau yana mai mika godiya ga shugaban kasa da ya saurari koken al'umma, baya ga nuna godiya ga babban lauya Femi Falana da ya jagoranci kare yaran da ma sauran abokan aikınsa kama daga Barr. Hamza Dantani, Barr. Deji Adeyanju da sauran su.

Sauari cikakken rahoto daga Halima AbdulRauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Yi Fatali Da Shari’ar Yara Masu Zanga-Zanga Da Aka Tsare Na Kusan Kwana 90.mp3