Wata kotun shari'ar Musulunci da ke birnin Kano a arewacin Najeriya ta yankewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke hukuncin ne sakamakon samun shi da ta ce ta yi da laifin yin batanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W.)
A cewar kotun, yayin wa'azinsa, Abduljabbar ya aikata laifuka da dama da ya cancanci hukuncin kisa.
Alkalin kotun Sarki Yola ya ce, ya samu Abduljabbar Kabara da laifin yi wa ma'aiki kage da cin mutunci.
An same shi da laifi karkashin sashe na 382 B cikin baka, dalilin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun har ila yau, ta ba da umarnin kwace masallatansa guda biyu, tare da haramtawa kafofin yada Labarai na jihar Kano sanya wa'azinsa.
Wannan hukunci dai ya biyo bayan gaza kare kansa da malamin ya yi, bayan shafe kusan shekaru biyu da kotun ta yi ana sauraren laifin nasa.
“Mu masu gabatar da kara a madadin gwamnatin jihar Kano, mun kawo shaidu guda hudu, domin mu tabbatar da cewa ya aikata wannan laifi. Dukkan abin da aka zarge shi da su, kotu ta same shi da laifukan.” In ji Lauyan gwamnati Farfesa Mamman Yusufari.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, a lokacin da kotu ta ba lauyan da ke kare Abduljabbar dama ya yi magana, Barrister Aminu Ado Abubakar, ya nemi kotun da ta yi masa sassauci.
Amma da aka ba shi dama ya yi, Sheikh Abdujabbar ya ce bai san lauyan ba, yana mai cewa sai a ranar ya fara ganin shi.
Saurari jawabin lauyan gwamnati, Farfesa Mamman Yusufari:
Your browser doesn’t support HTML5