"Kotu ta bada umarnin a dage kariyar Mohamed Bazoum," in ji Abdou Dan Galadima, shugaban kotun, wanda sabuwar gwamnatin soji ta kirkiro a watan Nuwamba.
Hukumomin Nijar na zargin Bazoum da laifin cin amanar kasa, da ba da daukar nauyin ta'addanci.
An tsare shi a fadar shugaban kasa tare da matarsa Hadiza tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Bayan an kammala sauraron karar na ranar Juma’a, Ould Salem Mohamed, daya daga cikin lauyoyin Bazoum, ya ce za su yi la’akari da hukuncin, kuma tawagar lauyoyin kariya za su ba da sanarwa nan ba da jimawa ba.
Ana zargin Bazoum ne da yin magana ta wayar tarho da shugaban Faransa Emmanuel Macron da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a yunkurin neman goyon bayansu a lokacin juyin mulkin.
An dage zaman kotun har sau biyu, yayin da lauyoyin Bazoum suka koka kan wasu matsaloli da suka ce ya kawo cikas ga ‘yancin kare hambararren shugaban.
A watan Disamba, kotun kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta ba da umarnin a sake shi ba tare da bata lokaci ba.
Wata guda bayan umarnin, Nijar ta fice daga kungiyar.
Your browser doesn’t support HTML5