A Africa ta Kudu ana sa ran shugaban kasar Jacob Zuma zai biya rabin dala milyan daya, ga asusun gwamnatn kasar, bayan kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa tilas shugaban ya biya wani kaso na dala milyan 16 kudaden gwamnati da aka yi amfani da su wajen sake gyara gidan Zuma na kansa a garin da ake kira Nkandla.
WASHINGTON DC —
Haka nan kotun ta bukaci sashen Baitulmalin yayi kiyasin nawa shugaban kasan zai biya saboda gyare-gyaren da aka yi a gidan nasa. Mr. Zuma yana da kwana 45 ya biya wadannan kudade.
Dan majalisa daga bangaren 'yan hamayya na jam'iyyar DA Jordan Lewis, yace sun yi na'am da wannan hukunci.
Ahalinda ake ciki kuma, an rantasarda sabon jakadan Amurka a Somalia Stephen Schwartz, mataki da ya sa ya zama jakadan Amurka na farko cikin shekaru 25, wanda hakan wani babban mataki ne a dangantakar Amurka da Somalia.
Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken wanda ya jagoranci bikin rantsuwar kama aikin, yace Somali tayi namijin kokari wajen sake farfado da kasar.