Kotun dake zamanta a birnin Lagos ta yanke hukunci kan wasu kamfanoni guda Hudu dake da alaka da Madam Patience Jonathan, inda aka samesu da laifin karkatar da wasu makurdan kudi har fiye da Dalar Amurka Miliyan 15, kwatankwacin Naira Biliyan 70.
A hukuncin da alkalin kotun Justice Babs Kuewumi ya zartar ya bayyana cewa ya gamsu da hujjojin da hukumar EFCC ta gabatarwa kotu dake nuna cewa lalle kamfanonin na da hannu wajen batar da kudaden da ake ganin an sato su ne daga Baitulmalin gwamnati.
Tun da farko dai kamfanonin Hudu sun amsa laifukan da ake tuhumarsu ta hannun wasu daraktocin kamfanonin. An dai yankewa kamfanonin hukuncin ne tare da wani tsohon mai taimakawa Goodluck Jonathan mai suna Waripamo-Owei Dudafa wanda ke zama lauya.
Kwamred Abdulsalam Abubakar, mai rajin fafutukar kare ‘yancin bil Adama, yace wannan hukunci da kotu ta zartar yayi kyau kasancewar bai dauki lokaci mai tsayi ba. sai dai kuma kotun tace a watan gobe ne zata ajiye ranar da zata zartar da irin hukuncin da ta yanke akan wadanda ake zargin, na aikata laifin karkatar da dukiyar kasa.
Tuni dai matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan, ta kai karar hukumar EFCC da kuma bankin Sky Bank wadanda take zargi sun bayyana asirinta tare kuma da dagewa kan cewa kudaden da ake zarginta da wawure kudaden ta ne da ta mallaka.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5