Kotun da ke sauraron karar da almajiran Sheik Ibrahim Zakzaky suka shigar a Kaduna, ta dage zamanta a yau Litinin zuwa ranar Litinin ta makon gobe.
Mai Shari'a Darius Khobo na babbar kotun Kaduna ne ya dage karar zuwa 5 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan bukatar El Zakzaky ta zuwa kasar wajen domin neman magani.
Barista Sadau Garba, lauyan da ya yi magana a madadin bangaren Sheikh El Zakzaky, wanda shi ne shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) a Najeriya, ya ce bukatarsu ita ce a saki malam ya tafi neman magani.
Lauyoyin malam El Zakzaky na so ne a fita a shi kasar waje don ganin likita, matakin da hukumomin jihar ba su yi na'am da shi ba.
Lauya Bayero Dari, wanda ya wakilci gwamnatin jihar Kaduna a zaman kotun na wannan rana, ya ce kotun ta saurari dukkan koken da aka kawo, kuma za'a duba sannan a yanke hukunci.
Yadda Aka Tsaurara Matakan Tsaro a Kaduna
Sanadiyyar sauraren wannan kara, a yau hukumomin tsaron a jihar ta Kaduna sun tsaurara matakan kariya inda aka rufe wasu hanyoyi, lamarin da ya haifar da cunkoson ababan hawa.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da cewa shari'ar jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Sheik Ibrahim El-zazzaky ce ta sa aka rufe wasu hanyoyi a garin Kaduna don gudun tashin hankali.
A yanzu dai garin Kaduna ya samu natsuwa bayan dage karar da kuma janye jami'an 'yan sanda akan hanyoyin.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5