A ranar Juma’a Alkali Okon Abang na kotun tarayya da ke Abuja ya ba da umurnin da a tsare Maina a gidan kurkuku da ke Kuje da ke birnin.
Hakan na faruwa ne kwana guda bayan da ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka tiso keyar Maina daga Jamhuriyar Nijar inda rahotanni suka kokari ne na tserewa.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lauyan Maina, Francis Orusanya ya janye daga shari’ar, lamarin da ya sa sabon lauyansa Abel Adaji ya nemi a dage karar don ya samu damar yin nazarin al’amarun da suka wakana a shari’ar.
Maina na fuskantar tuhume-tuhume 12 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke yi masa wadanda suka shafi karkata akalar kudaden kwamitin na fansho da ya jagoranta.
A farkon makon nan aka gano Maina ya yi kokarin tserewa bayan da aka gano shi a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriyar.
Kusan makonnin biyu da suka gabata, Alkali Abang ya sa aka tsare Sanata Ali Ndume a gidan yari har na tsawon kwana biyar, bayan da ya kasa kai Maina gabanta.
Ndume shi ya tsayawa Maina aka ba shi beli a wancan lokaci bisa sharadin zai kai shi a duk lokacin da ake bukatarsa.