Kotun koli a birnin Tarayyar Najeriya Abuja, ta yanke hukuncin mayar da tubabben mataimakin gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Sani Danladi a matsayin gwmanan Jihar.
WASHINGTON, D.C —
A halin yanzu dai an girke jami’an tsaro a cikin birnin Jalingo domin gudun tada zaune-tsaye.
Cikin shirin ko-ta-kwana, domin gudun abunda ka iya faruwa, a birnin Jalingo bayan hukuncin da kotun kolin ta yanke Juma’arnan, inda ta bukaci a hanzarta rantsar da tsohon mataimakin gwamnan Jihar, Alhaji Sani Danladi da ‘yan majalisar dokokin jihar suka tsige a baya.
Barrista Solomon Dalung, na daga cikin lauyoyin da suka wakilci Alhaji Sai Danladi.
“Ainihin kwayar magana, itace a bi ka’ida, yanda tsarin mulki ya shimfida, idan tsige shi za’a yi. Abunda muka kalubalanta kennan”, inji Dalung.
Yanzu haka wannan hukunci ya raba hankulan al-ummar Jihar tsakanin masu murna, da wadanda ke takaici.
Your browser doesn’t support HTML5