Ana wannan shari’a ne tsakanin Maryam Sanda da kwamishinan ‘yan sandan birnin Abujar Najeriya bisa zargin ta kashe mijinta Bilyaminu Muhammed a ranar 19 ga watan Nuwambar da ya gabata. Da farko Alkalin babbar kotun mai shari’a Halilu Yusuf ya karantowa Maryam laifin da ake tuhumarta da shi na kashe mijinta Bilyaminu, ya kuma tambayeta ko ta amince da laifinta?
Nan take Maryam dake sanye da Koriyar atamfa, ta kume rufe fuskarta tana rike da carbi a hannunta, tace bata amince ba. Sai kuma mahaifiyar Hajiya Maimuna Sanda da yayan Maryam din wato Aliyu Sanda da kuma wata ‘yar aikin gida mai suna Sadiya Aminu, da su kuma ake tuhumarsu bisa zargin lalata shaidar zargin da ake yiwa Maryam.
Ta hanyar goggoge jini da sauran abubuwan da aka iya zama shaida a wannan shari’a da ake yi a halin yanzu. Su ma duk sun ki amincewa da zargin da ake yi masu. Lauyan Maryam Sanda, kuma babban Lauyan Najeriya JB Daudu ya nemi kotu ta bada belin Maryam Sanda bisa koken cewa, bata da lafiya da ma sauran mutane uku da ke fuskantar shari’ar.
Bayan an dage zaman kotun na kimanin sa’o’i uku, mai shari’a Halilu Yusuf ya zartar da hukuncin cewa, ba za a bada belin Maryam ba saboda Kotu bata gamsu da hujjojin rashin lafiyar data gabatar ba, amma kotu ta bada belin mahaifiyar Maryam din da yayanta da ita kanta 'yar aikin tata bisa wasu sharudda.
Ga karin bayani cikin sauti a rahotonmu.
Your browser doesn’t support HTML5