Kudaden sun samo asali ne daga bashin Paris Club da gwamnati ta ciwo a madadin Jihohin.
Mai Shari'a Inyang Ekwo na babban Kotun Tarayya da ke Abuja ya hana gwamnatin tarayya cire wadanan kudaden ne, bayan lauyoyin da ke kare gwamnonin suka ce, jihohi za su shiga halin ha'ula'i idan an debe wadannan kudaden domin ko a yanzu, yawancin jihohin ba sa iya rike kansu. Amma Masanin tattalin arziki na kasa da kasa, Shuaibu Idris Mikati yana mai ganin gwamnati ba ta da laifi idan ta nemi kudaden da ta yi wa jihohi lamuni tunda jihohin ne suka mori kudaden.
To sai dai ga Malami a tsangayar Tattalin Arziki a Jami'ar Kashere ta Jihar Gombe, Dokat Isa Abdullahi, yana ganin matakin da kotu ta dauka akan wadannan kudaden ya yi daidai domin idan aka ce za a rika cire wadanan manyan kudade daga asusun jihohin kasar, musamman ma jihohin Arewa, ko albashin ma'aikatan su ba za su iya biya ba.
Amma a lokacin da yake nashi nazari masanin harkar hada-hada da musayar kudade Kassim Kurfi yana mai ra'ayin gwamnati tana da hurumin cire kudade daga cikin asusun jihohi domin akwai hakkin wadansu mutane a cikin kudaden ba ma na gwamnatin tarraiyya kawai ba.
Daga dukan alamu,wannan dadadar magana ce tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi tun lokacin da aka yafe wa Najeriya basusuka a shekarun baya, wasu suka yi kwangilar fitar wa jihohi kason su a zamanin wanan mulki na Shugaba Buhari, amma jihohin ba su biya yan kwangilan ba.
An daga sauraren karar har sai ranan 30 ga wanan wata da muke ciki.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5