Daga cikin sharuddan, an bukaci Ndume ya samu mutum day da zai tsaya masa wanda zai kasance yana da wata tsayayyar kadara a birnin na Abuja.
Sannan kotun ta kuma bukaci da ya mika fasfo dinsa ga hukumomi.
Lauyoyin Ndume Wanda ke wakiltar kudancin jihar Borno da ke area masa gabashin Najeriya, sun kwashe kwanaki suna kokarin nema masa beli a gaban kotun.
A ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba ne alkali Okon Abang ya ba da umurnin a tsare Ali Ndume a gidan yari akan tuhumar saboda ya gaza kai Abdulrashid Maina gaban koton saboda shi ya tsaya masa aka ba shi beli
Maina, shi ne tsohon shugaban tsohuwar hukumar kula da harkokin fansho a Najeriya wanda tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya nada a shekarar 2013.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta zarge shi da halatta kudaden haram har aka tsare shi a gidan yari aka kuma kwace masa wasu kadarori.
A wata hira da Muryar Amurka, Ndume ya tabbatar da cewa kasa kai Maina a gaban kotun ya sa alkalin ya bukaci a tsare shi, duk da cewa ya nemi a ba shi dama ya kare kansa amma alkalin ya ki.