Kotu Ta Gindaya wa Gwamnati Sharadi Kan Rike Kudaden Da EFCC Ta Gano

EFCC

Wata kotu a Jihar Legas ta umurci gwamnati ta rike makudan kudaden da aka gano a birnin a 'yan kwanakin nan ciki har da sama da dala miliyan 43 da aka bankado a wani gida dake yankin Ikoyi a farkon makon nan.

Alkalin kotun Justice Muslim Hassan ya ba gwamnatin tarayyar Najeriya umurni da ta ci gaba da rike kudaden har sai nan da makwanni biyu tare da yin shelar neman mai kudin.

Amma bayan makwanni biyu ba tare da wani ya gabatar da kansa ba a matsayin wanda ya mallaki kudin to ita kotun ta halartawa gwamnatin tarayya ta mallake kudaden.

Lauyan EFCC Rotimi Oyedepo shi ya gabatar da kudurin a gaban kotun yayin da ya gabatar da kara a madadin hukumar inda ya nemi a mallakawa gwamnatin tarayya kudaden.

Amma alkalin ya ba hukumar umurnin cewa ta tallata shelar neman mai kudaden a jaridu da sauran kafafan yada labarai har na tsawon makwanni biyu kafin gwamnati ta rike kudin idan har ba a sami mai su ba.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Gindaya wa Gwamnati Sharadi Kan Rike Kudaden Da EFCC Ta Gano - 1' 41"