Mai Shari'a, Nura Yusuf Ahmad, ya bada wannan doka ne a yau a yayin zaman kotu
Ya ce yadda wacce ake tuhuma ta bayyana a gaban kotu ya nuna cewar Murjar bata cikin hayyacinta, sakamakon tasirin miyagun kwayoyi
Kotu ta bukaci da cigaba da kulawa da Murja karkashin hukumar ta Hisbah har zuwa lokacin da sakamakon asibitin kwakwalar ya bayyana na tsawon watannin uku
Kotun za ta sake zaman ta ne a ranar 20 ga watan Mayu mai zuwa.
Da Muryar Amurka ke zantawa da Kakakin Kotuna ta jihar Kano Muzzamil Ado Fagge, ya ce dole a hukunta bayan samun sakamakon lafiyar ko akasin haka na kwakwalwarta da asibti, inda ya kara da cewa batu na ko ta yi haka ne domin samun sassauci sai ya ce lokaci zai bayyana gaskiyar ta ko akasin haka.
Muzammil ya ce mutane na ta yada jita-jitar cewar ta samu wani gata daga bangaren gwamnati, sai ya ce duk wannan labari ne ko a baya kotu ta hukunta Murja har ta yi zaman gidan gyara hali wanda ba ta canza ba.
A wannan karo ma zasu bi dukkanin dokokin da kotu ta gindaya har zuwa ranar da za’a sake sauraron ta idan aka kamata da laifi lallai zata fuskanci shari’ar dai dai da laifin da ta aikata.
Ya ce ta saba da al’ada da tarbiyar mutanen Kano, kuma dole a dauki mataki na abinda ya dace domin shiryar da kanta da ma al’umma da suke bibiyarta, ko a baya gwamnan Kano ya tambayeta ko tana da wanda ta ke so domin gwamnati ta yi mata aure.
Asibtin ne kadai zai bada tabbacin lafiyar kwakwalwar ta sannan da gwamnati nayi mata gata da ba’a kai da kawo Murja kotu ba domin a hukunta ta ba.
Dangane da jita-jita na cewar Kwamandan hukumar Hisban ya ajeyi mukaminsa sakamakon sakin Murja kafin sauraron kes din Murja, mataimakiyar Kwamandar Hisbah Dr Khadija Sagir ta sake mussanta hakan inda ta ce labari ne kagagge kuma babu kamshin gaskiya a ciki.
Saurari cikakken rahoton Baraka Bashir:
Your browser doesn’t support HTML5