Kotu Ta Bayar Da Umurnin Dakatar Da Gina Kasuwar Mpape A Abuja

Kasuwar Mpape Da Ke Abuja 1

Kananan ‘yan kasuwa da ke hada-hadar su a unguwar Mpape da ke gefen Abuja, inda talakawa su ka fi zama, sun kaure da murnar dakatar da mamaye musu kasuwa da kotu ta yi.

Alkalin babbar kotun Abuja da ke garin Bwari Mai shari’a Muhammad Madugu ne ya yanke hukuncin dakatar da gina kasuwar bayan ruguje ta a bara.

‘Yan kasuwar dai da su ka hada da maza da mata sun ce tun gurbin kasuwar na gona ko ma daji su ka fara gudanar da kasuwanci kafin karamar hukumar Bwari da yankin ke karkashinta ta bullo don kula da kasuwar bayan waje ya bunkasa.

Wata rana kwatsam kamar yadda muka taba kawo labari sai karamar hukumar ta turo motocin rushe gine-gine ta ruguje kasuwar da zummar gina sabuwa, inda daga bisani a ka damkawa wani kamfani SHAPE IDEAS aikin gina kasuwar da hakan zai sa sam asalin ‘yan kasuwa ba za su samu shagunan su ba.

Kasuwar Mpape Da Ke Abuja 2

Bayan yanke hukuncin dakatar da ginin shugaban ‘yan kasuwar Alhaji Saidu Abdullahi Rumo ya ce nasarar ta zama tamkar maidawa masu hakki kayan su ne.

Lauyan masu shigar da kara Sani Sajo ya zaiyana gina kasuwar ba da hannun ‘yan kasuwar ba ya sabawa dokokin mallakar kasa.

Har yanzu dai ‘yan kasuwar na rakubu a sauran gefen filin kasuwar da a ka ruguje su na kasa kaya kamar ‘yan ci rani.

Tsadar kasuwanni a Abuja ko hayar shaguna kan sa kaya na zama masu dan karen tsada in an kwatanta da wasu sassa wajen da kokuwar babban birnin.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Kananan ‘Yan Kasuwar Mpape A Abuja Sun Kaure Da Murna Bayan Umurnin Kotu.mp3