WASHINGTON, D. C. - Tun da farko dai shahararren ya ki amsa laifin cin zarafin Naira da ake tuhumar shi da aikatawa, a lokacin da ake shari’a.
An gurfanar da Cubana a gaban mai shari’a Kehinde Ogundare a kan tuhume-tuhume uku da suka shafi cin zarafin Naira ta hanyar yin like da kudi a wani taron jama’a, wanda hakan ya sabawa dokar babban bankin kasar (CBN) ta shekarar 2007.
Ana kuma zarginsa da yin like da Naira a ranar 13 ga Fabrairu, 2024, a Otal din Eko.
Haka zalika an ce Cubana Chief Priest ya aikata laifukan ne yayin da yake rawa a wani taron jama'a.
An ce ya yi ta’ammali da kudade na takardun Naira 500 da CBN ta fitar ta hanyar like da kudaden har na tsawon sa’o’i biyu.
A ranar 5 ga Afrilu, 2024, Hukumar EFCC ta yanke hukuncin dauri kan fitaccen mai shigar tufafin mata da maza, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, bisa irin wannan tuhuma aka kuma yanke masa hukuncin daurin watanni shida a ranar Juma’a, 12 ga Afrilu, 2024.
Ranar Lahadin da ta gabata ne dai hukumar EFCC ta bayyana cewa tana kuma binciken wasu fitattun jaruman da ake zargi da wofinta kudin Naira ta irin wannan hanyar.
A halin da ake ciki kuma, Jarumi Seun Jimoh ya zargi Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da muzantawa fitattun mutane yayinda ta ke neman inganta amfani da kudin kasar wato Naira.
Ya zargi hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da nunawa mashahuran mutane rashin adalci a ci gaba da dakile masu cin zarafin Naira.
Jimoh ya ce "ba daidai ba ne a ce ana zabar wasu mutane da aikata laifi bayan kusan kashi 70% na 'yan Najeriya ko fiye sun aikata wannan laifin da kuma Shaidar haka a bidiyo kan intanet."