Tawagar lauyoyin da ke kare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a karar da aka shigar da shi kan zargin yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W a Kanon Najeriya, ta ce ta janye daga aikin kare malamin da take yi a kotu.
Cikin wata wasika da suka gabatarwa kotun, Saleh M. Bagoro, H.G Magashi, Bashir Sabiu, R.S Abdullahi da Y.A Umar, sun ce sun yanke shawarar janyewa daga aikin kare shi ne bayan da suka tattauna da Abduljabbar a cewar jaridar Daily Nigeria.
Rahotanni sun ce tuni Alkali Ibrahim Sarki Yola da ke sauraren karar ya amince da janyewar lauyoyin.
Bayanai sun yi nuni da cewa, kotun ta ba malamin damar ya nemi wasu lauyoyi bayan da ya bukaci hakan.
A ranar Alhamis tawagar lauyoyin ta mika wannan bukata amma ba ta fadi dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki ba.
Janyewar lauyoyin na zuwa ne, yayin da aka gabatar da rahoton binciken lafiyar kwakwalwar Abduljabbar wanda ya nuna cewa lafiyarsa lau.
A kwanakin baya kotun ta ba da umarnin a gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwar malamin.
Alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa 30 ga watan Satumba.