Kotun daukaka kara da ke Yola karkashin jagorancin, Justice Chidi Nwaoma Uwa, ta dakatar da hukuncin farko da wata kotun tarayya ta yi a Jalingo wanda ya haramtawa dan takarar jam’iyyar APC, Sani Abubakar Danladi, shiga zaben gwamna da za a yi ranar Asabar 9 ga watan Maris.
An wanke dan takarar gwamnan daga karar da wasu mutanan jihar Taraba su hudu su ka shigar gaban kotun tarayya da ke Jalingo, suna zarginsa da yin karya wajan bayyana shekarunsa na haihuwa da na karatu da ya gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Taraba, Barr. Ibrahim El-Sudai, ya ce sun yi farin ciki da nasarar da suka samu, wanda kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin farko na kotun tarayya da ke Jalingo kuma yanzu haka ya ba su ‘yancin shiga zabe
Shi ma a nasa bangaren, Sanata Yusuf A. Yusuf, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya ce ba gudu ba ja da baya a zaben gwamnan da za’a yi gobe.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5