Kotu: Masarauta Daya Ce Kawai A Jihar Kano

Babbar kotun jihar Kano ta soke dokar da ta kafa sabbin masarautu guda hudu, wadanda aka kirkiro karkashin masarautar ta Kano.

A zaman kotun na yau karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na-Abba, kotun ta gamsu da hujjojin da tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dokokin jihar Kano Rabiu Sale Gwarzo ya gabatar a gabanta, na cewa an saba ka’idojin dake kunshe a kundin zartar da doka na Majalisar.

A watan Mayu da ya bagata ne Majalisar Dokokin ta Kano ta amince da gyran fuska, ga kundin dokar nada sarakuna a jihar Kano, wanda ya bada damar samar da sabbin masarautu hudu a jihar Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Sanusi Lamido Sanusi III, da Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje

Wadanda aka shigar da karansu gaban kotun, sun hada da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da shugaban Majalisar Dokokin jiha da ofishin Atoni Janar da kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano.

Da yake zartar da hukunci game da karan, alkalin kotun mai sharia Usman Na Abba, ya ce hanyoyin da Majalisar ta bi wajen samar da dokar da ta kafa sababbin masarautun cike suke da kura-kurai don haka, kotun ta soke wancan gyaran.

Saurari rahoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu: Masarauta Daya Ce Kawai A Jihar Kano