Kotu A Kano Ta Umarci Wasu Alkalai 2 Su Janye Daga Kwamitocin Da Aka Kafa Domin Bincikar Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

An nada alkalan kotunan Kanon guda 2 ne domin su shugabancin kwamitocin bincike akan dawo da dukiya da kadarorin al’umma da aka wawure da kuma binciken tashe-tashen hankulan dake da nasaba da siyasa da batan mutane.

Mai Shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya dake Kano ya bukaci Mai Shari’a Farouk Lawan Adamu da takwararsa Zuwaira Yusuf su janye daga zama mambobi a kwamitocin binciken da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa domin bincikar magabacinsa, Abdullahi Ganduje, cikin sa’o’i 48.

Gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamitocin 2 ne domin bincikar gwamnatin mutumin daya gabaceshi, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma shine shugaban jam’iyyar APC mai ci.

A yau Alhamis, Mai Shari’a Simon Amobeda, ya bada umarnin yayin da ya zartar da hukunci a karar da Ganduje ya shigar, inda ya bukaci kotun ta dakatar da Gwamna Abba daga bincikar gwamnatinsa.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu A Kano Ta Umarci Wasu Alkalai 2 Su Janye Daga Kwamitocin Da Aka Kafa Domin Bincikar Ganduje