Manzon Amurka na musamman a Kuriya ta arewa Stephen Bosworth zai gana da shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar Kuriya ta kudu, Wi Sung-lac a yau laraba a birnin Seoul.
Ana kyautata cewa za su maganta ne akan sharudan da ya kamata gwamnatin Kuriya ta arewa ta cika kafin a sake tattaunawa da ita a kan raba ta da makaman nukiliya, sharudan sun hada da dakatar da shirye-shiryen ta na nukiliya da kuma barin jami’an binciken kasa da kasa su sake komawa kasar.
Da ya isa kasar Kuriya ta kudu a jiya talata, Bosworth ya yi kiran cewa tattaunawa da gaske gadan-gadan ne babban shirin da zai shawo kan kasar ta kwaminisanci.
Tattaunawar da kasashe shidda ke yi a kan raba Kuriya ta arewa da makaman nukiliya ta cije, amma a kwanan nan gwamnatin kasar Kuriya ta arewar ta nuna alamu, ta na da aniyar so a ci gaba da tattaunawar.
Bosworth ya yi wannan tafiya ce wadda za ta kai shi har kasashen China da Japan, a gabannin wani taron kolin da za a yi tsakanin shugaban Amurka Barack Obama da shugaban kasar China Hu Jintao a ranar 19 ga watan nan na janairu a nan birnin Washington, D.C, inda ake kyautata cewa kasar Kuriya ta arewa ce babban abun da za su tattauna a kai.
A jiya talata, shugaba Obama ya gana da ministan harakokin wajen kasar China, yang Jiechi wanda ya zo nan birnin Washington domin share fagen ziyarar da Mr.Hu zai kawo.