Gwajin harba makami mai linzami, mai cin dogon zango da Korea ta Arewa ta yi kwanan nan ya kara zafafa zaman dar-dar, yayin da kasar ta sanar cewa yanzu makamanta za su iya kai wa ko ina a Amurka.
Wannan shi ne gwaji na baya-bayan nan cikin watanni biyu da kasar ta yi.
A yau Laraba wani mai sanarwa a talabijin na KRT, mallakar gwamnatin Koriya ta arewa, ya bayyana gwajin makamin.
“An samu nasarar gwajin harba sabon makami mai linzami mai cin dogon zango samfurin Hwasong-15, wanda aka kera bisa shawarar Jam’iyyar Ma’aikata ta Koriya.”
Biyo bayan gwaje-gwajen makaman da Koriya ta arewa ta yi a baya, kasar ta yi ikirarin cewa makaman ta za su iya dira kan kowanne bangaren Amurka.
Amma wannan shi ne karon farko da kasar ta iya cimma haka da sabon makamin da ta kera.
Jami'an Amurka da na Korea ta Arewar sun amince da cewa makamin zai iya yin tashi mai nisan da ya fi wadanda kasar ta gwada harbawa a baya.