Wani harin kunar bakin wake da aka kai a gabashin Afgahnistan, ya halaka mutane takwas a jiya Alhamis, sannan ya jikkata wasu 16.
Jami’ai sun ce bam din wanda ya fashe a Jalalabad, hedkwatar Lardin Nangarhar, ya tarwatsa wani taron jama’a a wajen gidan wani tsohon kwamandan ‘yan sandan yankin.
Wani kakakin gwamnatin Lardin mai suna Attullah Khogyani, ya ce wadanda harin ya rutsa da su magoya bayan tsohon kwamandan ‘yan sandan ne, wadanda suke neman a mayar da shi kan mukaminsa.
Kungiyar IS ta yi amfani da kafar yada labaranta ta Amaq, ta ce ita ce ta kai wannan hari, tare da yin ikrarin cewa ta kashe mutane sama da mutane 50 a harin.
Facebook Forum