Korea ta Arewa ta sake cilla wasu makamai masu linzami da safiyar yau Talata, sannan kuma ta hada da jan kunnen makwabciyarta Korea ta kudu da cewa za ta iya daukar matakai don nuna rashin jin dadinta da atisayen hadin gwiwa tsakanin sojojin Korea ta Kudun da na Amurka da aka soma a cikin wannan makon.
Ofishin babban hafsan sojan Korea ta Kudu ya ce Koera ta Arewa ta cilla wadannan makaman masu linzami masu cin matsakaicin zango guda biyu, zuwa yammacin kasar.
Ya kuma kara da cewa makamin ya yi tafiyar nisan kusan kilomita 450 sannan ya tashi sama zuwa cikin sararin samaniya, inda ya yi tafiyar kilomita 37.
Sau hudu ke nan, Korea ta Arewa tana gwajin makamin cikin kasa da makonni biyu irin wadannan makaman masu linzami da ke da gajeran zango guda hudu ne, abin da ya janyo shakku game da tattaunawar da aka so su yi a cikin watan da ya gabata.