Komai Zai Tsaya Cik Ranar 16 Ga Watan Oktoba a Najeriya - TUC

Ma'aikatan Najeriya Yayin wata zanga zangar da suka yi a baya

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago ta Najeriya Ta yi Barazanar tsunduma cikin yajin aikin gama-gari muddin hukumomin kasar bas u fara aiwatar da matsayar da aka cimma b akan biyan albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.

Kungiyar ta TUC, ta sha alwashin kassara harkokin kasar baki daya a ranar 16 ga watannan nan Oktoba idan har ba fara biyan sabon albashin ba.

A baya hukumomin kasar da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya kan wannan albashi, amma bayanai na nuni da cewa, har yanzu ba a fara aiwatar da sabon tsarin ba a mafi aksarin jihohin kasar.

“Yajin da za mu shiga ranar 16 ga watan nan, yajin gama-gari ne, gabaki daya ma’aikatan Najeriya za mu tabbatar ba su fito aiki ba.” Inji mukaddashin Babban Sakataren kungiyar kwadago ta TUC a Najeriya, Comrade Nuhu Toro a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

Ya kara da cewa, “filayen jiragen sama insha Allahu za mu durkusar da su, wautar lantarki ba za a same ta ba, sannan har Fadar shugaban kasa ba za a samu wutar lantarki ba.”

Su dai ma’aikatan na Najeriya na so ne a fara biyan Naira 30,000 a matsaryin albashi mafi karanci kamar yadda aka yi yarjejeniya da su da gwamnati.

Gwamnatin shugaba Buharin dai ta ce ta ware sama da Naira biliyan 500 a cikin kasafin kudin badi domin biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina domin jin kari bayani: