Kwamared Abdulmajid Babangida Sa’ad shugaban Kungiyar masu fafatukar tattabar da shugabanci na kasa - ya ce matasa na sa ran cewar za’a yi musu kyaukyawar shimfida ta fannin ilimi, tattalin arzikin kasa da kuma magance musu matsalolin dabar siyasa.
Kwamerad Abdulmajid ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir dangane da tsammanin matasa a wannan sabuwar gwamnati da aka kafa.
Ya ce nisanta dabar siyasa na da matukar muhimmanci domin ta dabar siyasa anyi asarar dukiyoyi, da ma matasa sannan matasa na bukatar wannan sabuwar gwamnati ta magance wadannan matsaloli tare da kawo wa matasa dauki.
Ya kara da cewa a wannan karo ya kamata gwamanti ta kawar da wannan matsala sannan ta ja su a jiki tare da koyi da sauran sassan duniya na yadda ta ke tafiya da matasa wajen inganta ci gaban kasar su.
Ya ce kawo yanzu wannan sabuwar gwamnati ba za’a iya yi mata hasashe ba ko da ya ke ya a wancan zango bata yi wani abin azo a gani ban a irin rikon da ta yi wa matasa amma kwamared Abdulmajid na sa ran zata inganta a wannan zango.
Matasa na samun koma baya a kan dukkanin abubuwa da ta shafi rayuwar , ilimi tattalin arziki da kuma demokradiya , har kawo yanzu ba’a sakarwa matasa ragamar mulki ba.
Your browser doesn’t support HTML5