Kofi Annan Ya Ziyarci Kasar Myanmar A Kokarin Kawo Karshen Tashe Tashen Hankula

Tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya tabbatarwa al’ummar kasar Myanmar (ko kuma Burma) cewa, ba ya je kasar ne don ya kare hakkin bil adama ba, sai dai ya je ne don ya bada shawarwari akan yanda za a rage rigingimu dake tashi tsakanin Musulmi da mabiya addinin Buddha

A wani taron manema labarai da yayi jiya Lahamis a Yango, Kofi Annan yace basu zo kasar a matsayin jami’an bincike ko ‘yan sanda ba. Yace sun zo ne don su bada gudunmuwa a bisa gayyatar gwamnatin kasar ta Burma.

Darururwar masu zanga zanga ne suka tarbi dan asalin Ghana Kofi Annan a cikin fushi, a lokacin da ya isa jihar Rakhine dake yammacin Myanmar a farko wannan mako a matsayin daya daga cikin tawagar mutane tara masu neman hayoyin da za a kawo karshen rigingimun kablinaci da na addini masu tsanani da suka jefa al’ummar kasar cikin wahalololi masu yawa.

Masu zang zangar sun taru a wajen filin saukar jirage a babban birnin na Rakhine, inda suke nuna fushin cewar ‘yan kasashen waje na tsoma baki acikin matsalolinsu na cikin gida.

Shi dai wannan komiti na musamman mai bada shawara, wanda ya hada da yan asalin Myanmar guda shida da yan kasashen waje uku amma babu musulmi a ciki, yana kokarin nemo hanyar magance tashe tashen hankula da barke tun 2012 a lokacin da fadar ta kaure tsakanin mabiya addinin Buddha masu rinjayi da Musulmi da aka rinjaya.